ABNA24 : A wata sanarwa da sakatariyar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a wannan Litini, ta ce sam babu kamshin gaskiya game da wannan labarin, tana mai kuma nuna matukar bacin ranta kan labarin da ta ce marar tushe ne.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Nijar na nan kan bakarta na goyan bayan al'ummar musulmi musamman kungiyar hadin kai ta kasashen musulmi ta (OIC) ko (OCI) wacce za ta karbi bakuncin taron ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar karo na 47, da zai gudana a cikin wannan wata a Yamai babban birnin kasar.
Gwamnatin ta Nijar ta kuma yi tuni da cewa har kullum tana kan matsayinta game da rikicin Isra'ila da Falasdinu na goyan bayan kwamitin AL QODS AL SHARIF, wanda take a matsayin mamba a cikisa tun bayan kafa shi a cikin shekara 1975.
A kwanan ne dai wasu kafofin yada labarai na gabas ta tsakiya suka rawaito wani labari daga wata jaridar Isra'ila da ke cewa, Mahukuntan yahudawan na gudanar da wata tattauna ta sirri da Jamhuriyar ta Nijar da nufin dawo da huldar diflomatsiyya a tsakaninsu.
342/